Wike Bai da Abun Taimakawa Tinubu da Shi Don Lashe Zabe – Dakuku Peterside

 

Sabanin rade-radin da ke yawo, babban jigon APC a jihar Ribas, Dakuku Peterside, ya ce ba shi da masaniya kan cewa Wike na goyon bayan Tinubu.

Peterside wanda ya kasance tsohon darakta janar na hukumar NIMASA ya kuma ce Wike bai da abun taimakawa Tinubu da shi don lashe zabe.

Tsohon shugaban na NIMASA wanda ya kasance na hannun damar Rotimi Amaechi ya kuma ce Wike bai da tasiri a siyasa kawai kame-kame yake yi.

Rivers – Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Dr Dakuku Peterside, ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike bai da shaharar da zai iya taimakawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Bola Tinubu, a jihar Ribas.

Peterside wanda ya kasance tsohon darakta janar ha hukumar NIMASA ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da jaridar Punch ta wallafa.

Ana dai ta rade-radin cewa Wike, wanda shine jagoran gwamnonin G5 yana goyon bayan Bola Tinubu.

Sai dai kuma, da aka tambaye shi ko yana sane da cewar Wike na goyon bayan Tinubu, Peterside ya ce:

“Ba ni da masaniya. Na san cewa akwai rashin jituwa da rabuwar kai a tawagarsa a Ribas. Ina mai tabbatar maku, Wike na kame-kame ne kuma ba zai kaucewa kowa a hanya ba.

“Goyon bayan da yake tunkaho da shi duk shirme ne, son a sani, ko wanda ake daukar nauyi a kafofin watsa labarai. Ya zata yana da wayo ne, amma a kullun rashin adalcinsa da rashin gaskiya kara fitowa fili suke yi.

“Halin da yake ciki a yanzu shine cewa ya kange kansa a wani lungu mai wuya sha’ani. Ina tausaya masa. Shakka babu yana bukatar taimako.”

Yakin neman zaben Tinubu: Wike bai da abun bayarwa, inji Peterside

Da yake ci gaba da magana, Peterside wanda ya kasance na hannun damar tsohon ministan sufuri kuma babban abokin adawar Wike a siysa, Rotimi Amaechi, ya ce gwamnan na jihar Ribas ba zai cancanci kowace jinjina ba idan Tinubu ya lashe zaben 25 ga watan Fabrairu.

Yan Najeriya sun yi martani

Iñyañgetok-Harry Utom-UbôkAbasi Sundae ya yi martani a Facebook:

“Idan Wike ya marawa Tinubu baya a Ribas, ba za mu zabi Simi Fubara a matsayin gwamna ba. Magana ya kare.

“Yana yakin son zuciya ne ba na daidaito ku ra’ayin kudu ba.”

Amabekee Elvis Chisa ya ce:

“Gwamna Wike na haka ramin binne siyasarsa ne. Ina ba shi tabbacin cewa huldarsa da APC zai dakushe shahararsa nan ba da jimawa ba da kuma moriyar jihar Ribas da ke ya ci a yanzu. Kuri’ata ta Obi da Datti ne.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here