Wike na Zargin Shugaban Jam’iyyar PDP da Almundahanar N100m
Gwamnan Wike ya sake dira kan shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, Sanata Iyorchia Ayu.
Gwamnan na Rivers ya sake fallasa sabuwar zargin rashawa cewa Ayu ya karbi N100m hannun wani gwamna.
Wike ya lashi takobin cewa ba zasu daina kira ga tsige Ayu ba ko da ko hakan zai kai ga faduwar PDP.
Port Harcourt – Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya sake tsokano shugaban uwar jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, kan zargin almundahanar da yayi masa a watan Satumba.
Read Also:
Wike ya kara yanzu da cewa Ayu fa ya karbi milyan dari hannun wani gwamna, sannan ya koma wajen kwamitin gudanarwa ya sake karban wani milyan dari.
Wike ya bayyana hakan yayin hira da yan jaridar ranar Juma’a a birnin Port Harcourt.
Karo na biyu, Gwamnan jihar Rivers ya hau minbarin fara tonon silili kan wasu jiga-jigan jam’iyyar Peoples’s Democratic Party PDP.
A cewarsa:
“Ayu ya karbi N100m hannun wani gwamna don aiki cibiyar demokradiyyar PDP, sannan ya koma wajen NWC ya sake karban N100m duk na aiki daya.”
“Idan ya karyata zan fada muku sunan Gwamnan da ya bashi kudin.”
“Baicin soyayyar da mukewa jam’iyyar nan, idan muka fadi wasu abubuwa, har ‘yayan Ayu sai sun guje masa.”