Yadda Wole Soyinka ya Siffanta Najeriya da Shekara 2020
Shahrarren ma’abocin kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya siffanta shekarar 2020 a matsayin shekara mafi cike da kalubale saboda irin matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta.
Ya kara da cewa halin da Najeriya ta shiga ya tsananta sakamakon rashin shugabancin kwarai daga wajen yan siyasa da Malaman addini.
Read Also:
Soyinka, wanda yayi jawabi a Booksellers, inda ya gabatar da sabon littafinsa da ya kwashi shekaru 40 yana rubutawa, rahoton Punch. Sunan littafin ‘Chronicles of the happiest people on earth,’ (Jerin mutane mafi farin ciki a duniya).
“Dubi ga irin rikice-rikicen da suka faru a 2020, abubuwa basu yi dadi ba. Wannan shekarar na yi cikin mafi muni da na san kasar nan,” Soyinka yace.
“Abubuwa sun kai matakin da baka san idan za ka je ka tsira ko za ka mutu ba. Kamar yadda na fada, ba zaka yarda akwai wani shugaba a kasar nan ba.”