Gina Wurin Kiwo: Ban Nemi N6b Daga Gurin Gwamnatin Tarayya ba, Kuma Bazan Nema ba – Gwamna Umahi
Gwamnatin Ebonyi ta ce ba ta goyon-bayan a ware fili domin ayi kiwon dabbobi.
Gwamna David Umahi ya musanya kalaman da suka fito daga bakin Garba Shehu.
Umahi yace bai nemi gwamnatin tarayya ta ba shi kudi ba, kuma ba zai nema ba.
Ebonyi – Mai girma Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ta aika masa da Naira biliyan shida.
Gwamnatin tarayya ta ce Ebonyi tana cikin jahohin da suka karbi kudi domin gina wurin kiwon dabbobi.
Da aka yi hira da shi a Channels TV, mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, yace jahar Ebonyi ta karbi kasonta na kudin.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna David Umahi ya na tabbatar da cewa ba ya goyon bayan jahohi su ware wasu filaye domin dabbobi su iya yin kiwo.
A wani jawabi da David Umahi ya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Agusta, 2021, yace jahar Ebonyi ba ta da wani wurin da za ta iya ware wa makiyaya.
Jawabin gwamnan ya fito ta bakin mai ba shi shawara na musamman wajen yada labarai, Francis Nwaze.
“Mun samu labarin da ke zagaya wa cewa jahar Ebonyi ta na cikin jahohin tarayyar da aka ba Naira biliyan shida domin a samar da wurin kiwon dabbobi.”
“Ana alakanta wannan magana da hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, lokacin da yake amsa tambayoyi a tashar Channels TV a daren Laraba.”
“Gwamnatin Ebonyi ba ta taba neman kudi domin gina wuraren yin kiwon dabbobi ba, kuma ba za ta taba neman kudin da wannan manufar a jahar ba.”
Sanarwar ta kuma ce duk mai neman ya yi kiwon dabbobi a Ebonyi, ya yi wannan dawainiya da kansa cikin filinsa domin gwamnati ba ta da filin da za ta bada.