Raunin Gwiwarsa: Granit Xhaka Zai yi Jinyar Watanni 3

 

Granit Xhaka zai yi jinyar watanni uku saboda rauni da ya samu a gwiwarsa a wasansu da Tottenham Hotspur ranar Lahadi.

An canza kyaftin din na Arsenal dan kasar Switzerland a minti na 82, a wasan hamayya da suka doke makwabtansu Tottenham Hotspur 3-1.

Xhaka ya fara a wasanni hudu daga cikin shida da Arsenal ta buga a gasar Premier League ta bana, kuma bai buga wasanni biyu ba saboda jan kati da ya karba a wasan da suka buga da Manchester City ranar 28 ga watan Agusta.

A ranar Asabar ne Arsenal za ta je Brighton & Hove Albion a gasar Premier League, kuma za ta yi kokarin lashe wasa na hudu a jere, bayan rashin nasara a wasanni uku na farkon kakar bana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here