Rahotannin da Ake Yadawa a Kafafen Yada Labarai na Cewa PDP ta Zabi Wike Kawai Jita-Jita ne – Debo Ologunagba
A dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke jiran a bayyana gwamnan Rivers, Nyesom Wike a matsayin mataimakin Atiku Abubakar, jam’iyyar PDP ta fasa kwai.
A wani sako daga jam’iyyar a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni, sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo ya bayyana cewa ba a zabi Wike ba.
Ologunagba, ya ce ikirarin cewa an riga an zabi Wike a ga tafiyar karya ne domin har yanzu dai ana ta shawari a kai.
Abuja – Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da rade-radin da ake yi cewa kwamitinta ya zabi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
Read Also:
Vanguard ta ruwaito cewa, kwamitin zaben na jam’iyyar PDP, ya yi taro a jiya, domin cika aikin da ya rataya a wuyansa na ba da shawarar kan abokin tafiyar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.
Da yake magana kan wannan lamari a Abuja, Laraba, Sakataren Yada Labarai na kasa na PDP, Debo Ologunagba, ya ce rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa PDP ta zabi Wike kawai jita-jita ne.
Ya ce a halin yanzu kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar na duba lamarin tare da tuntubar juna, domin duba wanda ya fi kowa cancanta ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2023.
A halin da ake ciki, Ologunagba, wanda ya jaddada cewa PDP ta fara gudanar da ayyukanta na tantancewa, ya sanar da cewa za a yi taro a yau Laraba da karfe 11 na safe, inda ya ce ana sa ran za a duba kwamitin da ke shawari kan lamarin.