Yadda Za’a Dakile Harin ‘Yan Bindiga a Makarantu – Gwamna El-Rufa’i

Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya bayyana wasu abubuwa da ya dace ayi domin dakile harin yan bindiga a makarantun jahar.

Gwamnan ya ce ya kamata a samar d sansanin sojoji kusa da makarantu sannan a yi katanga a makarantun musamman na kwana da ke kauyuka.

Har wa yau, gwamnan ya ce akwai bukatar a kara adadin jami’an tsaro da ke jahar domin aikin ya fi karfin wadanda suke jahar a yanzu.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bada shawarar cewa a rika gina makarantu kusa da sansanin sojoji domin kare harin yan bindiga a jahar, The Cable ta ruwaito.

Yayin da ya ke magana a shirin gidan talabijin na kasa, NTA, a ranar Juma’a, El-Rufai za a iya dakile harin idan sojoji za su iya isa makarantun cikin mintuna 30.

A ranar Talata, an sace dalibai daga wata jami’a mai zaman kanta da ke Kaduna, wannan shine hari na uku da ake kaiwa makarantun jahar a wannan shekarar.

El-Rufai ya ce jahar na cigaba da aiki kan matakan dakile wasu hare-haren a gaba ciki har da ware kudade don gina katanga a makarantu.

Ya kuma ce Kaduna na bukatar karin sojoji a wuraren da abubuwan ke faruwa domin kallubalen tsaron ya fi karfin yan sanda da jami’an tsaro na Civil Defence wato NSCDC.

Gwamnan ya zayyana matakai uku da jahar za ta dauka don dakile hare-haren na yan bindigan

1. Gina katanga a makarantu domin rashin katanga na saukaka wa bata gari yin kutse

2. Samar da karin jami’an tsaro da suka hada da sojojin, Civil Defence, Masu tsaro na sirri, yan sa-kai da wadanda za su rika sa ido domin su sanar da hukuma idan sun ga an kawo hari.

3. Samar da sansanin sojoji kusa da makarantu ta yadda sojoji za su iya isa makarantun cikin minti 30

El-Rufai ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa yan bindigan sun fi kai hari makarantun kwana da ke kauyuka sannan da dare suke kai harin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here