Yadda Gobara ta yi ɓarna a Kano
Jihar Kano – An samu tashin wata mummunar gobara a unguwar Rijiyar Zaki da ke cikin birnin Kano.
Mummunar gobarar wadda ta tashi sakamakon sauke tukunyar gas daga wata mota ƙirar Peugeot J5 ta ƙone shaguna, motocci, da ajujuwa da dama a ranar Lahadi.
Jaridar Leadership ta ce hukumar kashe gobara ta jihar Kano ce ta bayyana hakan a ranar Litinin, 21 ga Afrilu, 2025, a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Abdullahi, ya sanya wa hannu.
Yadda gobara ta yi ɓarna a Kano
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:53 na rana a ranar Lahadi, 20 ga watan Afrilu, lokacin da hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa.
Hukumar ta samu kiran gaggawar ne daga wani mazaunin yankin mai suna Hamza Muhammad, wanda ya sanar da cewa gobarar ta tashi a Kwanar Yan Kifi, Rijiyar Zaki.
An tura jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar, da kuma na ofisoshin Rijiyar Zaki da Bompai, nan take zuwa wurin don daƙile gobarar.
Read Also:
Da suka isa wurin, tawagar ta gano cewa gobarar ta mamaye bene na ƙasa mai faɗin kusan ƙafa 100 da 50, wanda ke ɗauke da shaguna guda uku a gaban ginin kuma ana amfani da shi a matsayin wurin kasuwanci da dama.
Ɗaya daga cikin shagunan, wanda dillalin gas ke amfani da shi, shi ne ake zargin gobarar ta samo asali daga cikinsa, lokacin da ake sauke tukunyoyin gas daga wata mota da ba a san lambar rajistarta ba.
Gobarar ta bazu cikin gaggawa, inda ta ƙone motoci guda biyu da aka ajiye a wurin, sannan ta lalata wata mota ta uku.
Haka kuma, ta yaɗu zuwa makarantar Young Marshall Science Academy da ke kusa da wajen, inda ta lalata ajujuwa bakwai, ofis guda ɗaya, da banɗaki guda biyu da ke cikin makarantar.
Hukumomi sun shawo kan lamarin
Jimillar shaguna uku, motoci biyu, da ajujuwa bakwai ne suka kama da wuta, yayin da wata mota guda ɗaya ta ƙone kaɗan.”
“Da taimakon Allah da kuma jajircewar ma’aikatanmu, an samu nasarar kashe gobarar gaba daya, hakan ya hana yaduwar wutar zuwa wasu shaguna, ajujuwa da wata mota guda ɗaya.”
– ACFO Saminu Abdullahi