Yadda Masu Garkuwa Suka Sace Daliban Jami’ar Greenfield Dake Jahar Kaduna

 

Rahoto ya bayyana yadda aka sace daliban jami’ar GreenField dake jahar Kaduna a jiya Talata.

An bayyana cewa, ‘yan bindigan sun harbe mai gadin makarantar a kokarinsa na rufa kofa.

An kuma ce, ‘yan bindigan sun tuntubi iyayen daliban da aka sacen sun nemi miliyoyin kudi.

Gaskiyar bayanai sun bayyana kan yadda aka sace dalibai da wata ma’aikaciyar jami’ar Greenfield daga harabar makarantar da ke Kasarami, wani yankin karamar hukumar Chikun da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Daya daga cikin daliban da sojojin Operation Thunder Strike suka ceto ya fadawa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar da ke tsakanin shekaru 17 zuwa 20 sun mamaye jami’ar da misalin karfe 9:30 na daren Talata.

Dalibin (wanda aka sakaya sunansa) ya ce ‘yan bindigan sun fito daga bangarori daban-daban na harabar da ke kusa da kilomita 34 da babbar hanya kuma suka fasa wasu kofofi don kai harin.

“Yan bindigan ‘yan samari ne masu shekaru tsakanin 17 zuwa 20 amma sun zo dauke da makamai, sun zo ne suna harbi a iska akai-akai.

“Sun buge wasu daga cikin daliban tare da musu rauni, suka kashe mai gadinmu kuma suka tafi tare da wasu abokanmu, ban san takamaiman adadin ba amma na san galibinsu ‘yan mata ne ciki har da mata mai kula damu.

“An harbe mai gadin ne lokacin da yake kokarin rufe kofa ga ‘yan bindigan don kare mu,” in ji shi.

Magatakardar jami’ar, Bashir Muhammad, wanda ya kasance a sansanin Operation Thunder Strike inda aka ajiye daliban da aka kubutar kafin a sako su ga iyayensu, ya ce ba zai yi magana a kan batun ba bisa umarnin Shugaban Jami’ar.

Amma ya ba da tabbacin cewa shugabannin makarantar za su yi magana a kan lamarin kafin ko ranar Juma’a idan za a tattara bayanan abin da ya faru.

Wasu daga cikin iyayen, wadanda suka ki yin magana da manema labarai, tuni masu garkuwar suka tuntube su don neman kudin fansa na miliyoyi, in ji The Nation.

Magatakardan ya kuma tabbatar da cewa an tuntubi iyayen don neman kudin fansa amma bai bayyana adadin kudin da aka nema ba.

Wasu iyayen daliban da aka sace a wurin da harin ya faru sun kasance cikin matukar damuwa yin magana. An gan su suna tattaunawa kan yadda za a ceci yaransu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here