Yadda Rundunar Sojojin Najeriya ta Kama ‘Yan Boko Haram a Jahar Kano

 

Hankulan jama’ar jahar Kano ya tashi bayan kama wasu mutum 13 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a Hotoro.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an fara gangami tare da sanarwar wanzuwar ‘yan Boko Haram din ne a kafafen sada zumunta.

Yankin Hotoro zuwa Eastern bye-pass ya kasance dandali tare da mafakar jama’a daga Borno kuma suna ta gina gidaje a wurin.

A cikin kwanakin karshen mako ne hankulan jama’a suka tashi a Hotoro ta arewa dake karamar hukumar Nasarawa ta jahar Kano bayan sojoji sun cafke wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.

Samamen da sojojin suka kai a daren Asabar sun dira wani sabon gida ne da aka gano cewa jama’an daga jahar Borno suka tare.

Kamar yadda takardar da aka fitar ta bayyana, an tabbatar da kama mutum 13.

Tun a farkon zuwan Boko Haram jahar Kano, Hotoro ce cibiyar ayyukansu kafin a tarwatsa su sakamakon kokarin jami’an tsaro da na mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda wani mazaunin yankin mai suna Malam Muhammed Amadi ya sanar, sojojin sun yi aikin ne ba tare da jan hankalin jama’a ba.

Ya ce sojojin sun isa gidan wadanda ake zargin wurin karfe 9:15 na dare inda suka zagaye tare da yin awon gaba da wasu ‘yan gidan.

Ya kara da cewa mutanen basu yi yunkurin gudu ko wani artabu da sojojin ba, hakan yasa ba a harba ko harsashi daya ba.

Aliyu Garba Hakimi wani mazaunin yankin ne kuma kamar yadda yace, ya fara jin wannan gangamin ne a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda yace, bai san abinda yasa aka fara gangamin ba amma daga bisani ya gano cewa wasu irin mutane daga Borno sun cika yankin.

“Duk da basu da rigima, amma yadda suke basu son kowa ya zama wani abu daban. Gaskiya an fara gangamin ne kuma mutane da yawa sun fara zama cikin rashin yadda da su,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here