Yadda ‘Yan Bindiga Sukai Garkuwa da Wasu Mutane
Yan bindiga sun sake yin garkuwa da wasu mutane 2 a Zamfarawa da ke jihar Katsina da daren Lahadi.
Wani mutum Hamisu Maikarfe ya bayyana cewa sun shigo suna harbe harbe kafin su kutsa gida su dauki kanin sa Nafiu da kuma wani mutum Mallam Khamisu Dan Agaji.
Shima wani da ya kubuta daga fadawa komar yan bindigar ya bayyana cewa shi ya fadawa yan sanda bayan da ya tsira daga yunkurin harbin da yan bindigar suka yi masa.
Anyi garkuwa da mutane biyu da daren Lahadi bayan da wasu yan bindiga suka kai hari Funtua da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai harin a unguwar Zamfarawa bayan ginin bankin manoma kan titin Bakori da misalin 11:00 na dare.
HumAngle ta ruwaito cewa maharan sun zo dauke da miyagun makamai akan babura, suna harbe harbe don tsoratarwa da kuma kashewa.
Read Also:
Wannan na zuwa ne awa 24 bayan jami’an sintiri da na yan sanda sun ceto fiye da yara 80 a Mahauta kuma kasa da sati biyu da yan ta’adda suka yi garkuwa da fiye da dari 300 a makarantar sakandire ta Kankara a jihar Katsina.
Hamisu Maikarfe, wani mazaunin Zamfarawa ya shaidawa yan jarida cewa “rundunar sun mamaye kauyen mu suna ihu da harbe harbe”.
“Sun rikita unguwar gaba daya kafin su shiga gidanmu su sace kani na, Nafiu. Sai suka kutsa daya bangaren suka yi garkuwa da wani Mallam Khamisu Dan Agaji,” a cewar Maikarfe.
Mazauna yankin sun ce maharan basu dauki lokaci ba kamar yadda suka saba tsorata mutane.
Musa Aminu, wani da ya kubuta daga fadawa hannun yan bindigar lokacin da ya ke dawowa daga cikin garin Funtua ya ce yan ta’addan sun harbe shi.
“Lokacin da na ke dawowa gida, na gansu da mugwayen makamai kamar zasu yaki. Sun harbe ni sai dai basu same ni ba ko kadan,” inji Aminu.
“A lokacin da na tsira, sai na shigar da rahoto ofishin yan sanda a Funtua kuma sun dauki mataki cikin kankanin lokaci.”
HumAngle ta ruwaito cewa yan sanda sun isa wajen jim kadan bayan tafiyar yan bindiga da wanda suka yi garkuwar.
Har lokacin hada wannan rahoto yan bindigar basu kira don neman wani abu ba.