Yaduwar Cutar Korona: Gwamnatin Tarayya ta Saka Doka

Gwamnatin Tarayya ta kafa wasu sababbin dokokin yaki da Coronavirus.

PTF sun wajabtawa mutanen Ingila da Afrika ta Kudu gwajin COVID-19.

Sai an tabbatar da lafiyar duk wanda zai shigo Najeriya daga kasashen nan.

Kamar yadda ake sa rai, gwamnatin tarayya ta kawo wasu sababbin matakai da za a bi domin takaita yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya.

Kamar yadda sanarwar da aka fitar ta bayyana, gwamnatin Najeriya za ta fara dabbaka wadannan matakai daga ranar 29 ga watan Disamba.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yakar COVID-19, PTF, ya fitar da sanarwar a dazu.

Daga yau ranar Talata, an wajabtawa duk mutumin da ya shigo Najeriya daga kasar Birtaniya ko Afrika ta kudu yin gwajin kwayar Coronavirus.

PTF ya ce sai an tabbatar duk wanda zai shigo Najeriya daga wadannan kasashe bai dauke da cutar COVID-19 da yanzu ta sake barkowa a Duniya.

Ga kadan daga cikin abin da sanarwar ta ke cewa:

“Kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar #COVID-19 ya shigo da matakai na musamman ga matafiyan kasar Birtaniya da kuma Afrika ta kudu.”

“Matafiyan da su ka fito daga wadannan kasashe biyu sai sun yi gwajin kwayar #COVID19 na PCR, sa’o’i 96 da shigowarsu Najeriya.” Inji kwamitin PTF.

Jawabin ya ce: “Sannan sai sun gabatar da takardun biyan kudin sake yin gwajin COVID-19 a Najeriya.”

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here