Fyaɗe: An Zargi ɓangarori da ke Yaƙi a Sudan da Cin Zarafin Mata
Wani sabon rahoto kan cin zarafi ta hanyar lalata a Sudan ya zargi ɓangarorin da ke rikici da juna da aikata fyaɗe a kan mata da ƴan mata waɗanda shekarunsu ba su wuce aƙalla tara ba a Khartoum, babban birnin ƙasar da kuma biranen Omdurman da Bahri.
Read Also:
Rahoton wanda hukumar kare hakkin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta fitar, ya zargi dakarun RSF da aikata cin zarafi yayin da suke iko da yankunan da ke makwabtaka da juna a birane da dama.
Rahoton ya kuma zargi sojojin da ke mulkin ƙasar da aikata fyaɗe a wuraren da suke iko da su musamman waɗanda suka kwace daga wajen dakarun RSF.
Sai dai dukkan ɓangarorin sun musanta zarge-zargen.
Human Rights Watch ta yi kira da aka kakabawa masu aikata wannan aika aikar takunkumi da kuma tura dakarun da za su riƙa kare fararen hula.