Ina da Yakinin Cewa Wata Rana Komai Zai Sauya Don Ci Gaba – Muhammadu Sanusi II

 

Tsohon Sarkin Kano kuma shugaban mabiya Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya ja hankalin ‘yan kasar kan cin mutunci shugabanni saboda hali na tsananin rayuwa da suke ciki a kasar.

A lokacin jawabi zuwa ga mabiya daga jahohi bakwai a arewa maso yammacin Najeriya, a Sokoto, Sunusi ya nuna cewa yana da yakinin wata rana komai zai sauya don ci gaba.

Sanusi ya kuma nemi hadin-kan al’ummar Musulmi da kuma shawartar kungiyoyin Musulmi domin gina makarantu da bijiro da tsare-tsaren karfafa gwiwa don dogaro da kai.

Sannan ya jadada da yin tuni cewa addinin Musulunci bai yarda da barace-barace ba, da kaucewa duk wasu ayyukan da zai jefa mutum cikin hadari.

Tsohon Sarkin ya kuma yi kira ga mutane da su kasance masu ibada bisa dacewa da dokokin Musulunci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here