Zaɓen 2027: Me ya sa ƴan Adawa Suka Zaɓi ADC?
Bisa ga dukkan alamu a Najeriya an kama hanyar gina babbar hadaka ta siyasa gabanin babban zaben kasar na 2027, bayan shigar tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar ADC.
Ana kallon hadewar Kwankwaso da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar da kuma Peter Obi, wadanda dukkaninsu sun tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023, a matsayin wani babban ci gaba a bangaren hamayya a Najeriya, kuma wani babban kalubale ga jam’iyya mai mulki.
Yayin da ake ganin cewa siyasar hamayya a Najeriya tamkar ta shude – ganin yadda ake ta sauya sheka zuwa APC mai mulki, wasu masana na ganin wannan sabuwar hadaka ta jam’iyyar ta ADC ka iya zama wani babban kalubale ga Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC a zaben 2027.
Haka kuma masanan na ganin siyasar hamayya a kasar wadda ta fi yawan jama’a a Najeriya za ta sake farfadowa fiye da yadda ba a zata ba.
Sai dai kuma masanan na ganin akwai sauran rina a kaba idan har jiga-jigan yan hamayyar na Najeriya suka kasa hada kansu domin mara wa dayansu baya kan manufar zaben 2027 da ta hada
Farfesa Tanko Baba na jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto yana daga cikin masu wannan hasashe, kamar yadda ya sheda wa BBC.
”Wannan wani sabon zubi ne a siyasar adawa a Najeriya, saboda shigar da wadannan jiga-jigan ‘yan siyasa da wasunsu da suka bijire ma PDp saboda rikicinta na cikin gida suka shiga jam’iyyar ta ADC,” in ji masanin.
Ya kara da cewa: ”Sabanin yadda ake ganin kamar siyasar adawa a Najeriya ta mutu ta wannan zai sa ma ta dawo da karfin da ba a zata ba.”
Read Also:
Dangane da yadda wasu ke ganin kan wadannan manyan jiga-jigai uku zai iya rabuwa ya kuma watsa tafiyar ta ADC idan an zo fitar da dantakararta na shugaban kasa na zaben 2027, Farfesan ya ce : ”To ai zai yi wuya daman a ce an irin wannan hadaka ba tare da an yi tattaunawa tare da cimma matsaya ba a bayan fage, kafin ma a dunkule waje daya.”
”Idan kuma ya kasance ba a yi wannan tattaunawa da yarjejeniya ba tun da farko to lalle za a iya samun rabuwar kai a gaba,” a cewarsa.
”Amma lalle wannan hadaka ta ADC ta girgiza APC kuma tana ci gaba da girgiza ta, saboda wani abu ne da za mu iya cewa kila ba su yi lissafin aukuwarsa ba zuwa yanzu.”
Malamin jami’ar ya yi bayani da cewa idan aka yi la’akari da karfin wadannan jiga-jigai na ADC, musamman a yankunansu to ba shakka, jam’iyyar barazana ce ga APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa na 2027.
Me ya sa ƴan adawa suka zaɓi ADC?
A watan Afrilun 2025 ne wasu jiga-jigan ƴansiyasa a Najeriya da ke hamayya da gwamnatin jam’iyyar APC suka amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama’iyyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.
Ƴansiyasar sun ce sun amince da ADC ne da nufin haɗa ƙarfi da ƙarfe a cikinta da nufin kawar da jam’iyyar APC daga mulkin Najeriya a zaɓen 2027.
An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar ranar Laraba 2 ga watan Yuli a babban ɗakin taro na Ƴar’adua Centre da ke birnin Abuja.
Sabuwar haɗakar ta ADC ta zaɓi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, wadda suka amince da ita a matsayin jam’iyyar haɗaka.
Ɗantakarar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, da na Labour Party, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na daga cikin mashahuran ƴan siyasa da suka shiga haɗakar tun farko.
Sauran ƙusoshin siyasar da suka shiga haɗakar sun haɗa da tsohon gwamnan Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na APC, da tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.















