Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Katsina
Awanni kalilan a tsakani, yan bindiga sun sake kai hari wani ƙauye kusa da babban birnin jihar Katsina, jihar shugaban ƙasa.
Yan ta’addan sun kashe mutum uku, sun kuma yi awon gaba da gomman mutane mata da kananan yara a ƙauyen Dantsauni, yankin Batagarawa.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Isah, ya ce mutum ɗaya aka kashe, wasu biyu kuma na kwance a Asibiti.
Katsina – Yan ta’adda da yawa ɗauke da muggan makamai sun sake kai hari Ƙauyen Ɗantsauni da ke ƙaramar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, inda suka kashe rayuka uku.
Ɗaya daga mutunen da suka kashe, Abdulrashid Abba Manna, mazaunin cikin garin Katsina ne, wanda ya je gonarsa da safe a kauyen, amma yan ta’adda suka rutsa shi suka kashe.
Read Also:
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan harin ya zo ne awanni kaɗan bayan yan bindiga sun shiga kauyukan Babbar Ruga, Kwarin Maikotso da Kore, inda suka ci karen su babu wanda ya tanka musu, suka kashe rayuka biyu.
Kauyen Ɗantsauna yana maƙwaftaka da Babbar Ruga, tsakanin su bai wuce tafiyar kilo mita ɗaya ba.
Yadda Sabon Harin Ya Faru A sabon harin, yan ta’addan sun sace gomman mutane da suka haɗa da mata da ƙananan yara yayin da ɗaruruwan mazauna suka tsere zuwa garin Katsina don tsira da rayuwarsu.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan bindiga sun buɗe wuta a kan hanyar Katsina wurin da babu wani nisa zuwa cikin birnin.
Mazauna sun ce ba su ga ko jami’in tsaro ɗaya ba lokacin harin yan bindigan waɗan da suka shafe mintuna sama da 45 suna aika-aika kuma da hasken rana.
Yayin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun hukumar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da harin da cewa an kashe mutum ɗaya wasu biyu sun jikkata.