‘Yan Arewa Sun Roki Pantami ya Kai Kukan su Gurin Buhari

 

Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, ya tayar da hankulan jama’a.

Jama’a da dama, musamman ‘yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman.

Wasu ma’abota amfani da dandalin sada zumunta na tuwita sun roki ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya isar da sakonsu ga Buhari.

Dakta Isa Pantami, ministan Sadarwa da tattalin arziƙin fasahar yanar gizo, ya ce zai miƙa saƙonnin jama’a ga Shugaban ƙasa Muhammad Buhari bisa kisan gillar da ƴan Boko Haram suka yi na manoma 43.

A jiya, asabar, ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, dake ƙaramar hukumar Jere, jihar Borno, sun bi manoma har gonakinsu sun yi musu yankan rago.

Sheik Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na sadarwarsa a manhajar Tuwita bayan wani mai amfani da shafin ya roƙe shi da yin hakan.

“Ya Sheikh @DrIsaPantami – muna kawo kukan mu gareka. Dan Allah dan Annabi ka samu ka yi ma shugaban qasa magana.

Mutum arba’in da uku (43), ko a fim aka kashe wannan adadi lokaci daya, abun zai bada tsoro. “Dan Allah a taimaka a yi wani abun a kai, abun ya fara yawa.

#ZabarmariMassacre”.

Shi kuma Pantami sai ya mayar masa da martani cikin harshen turanci kamar haka.

“Muna ta yin hakan, kuma zamu cigaba da yin hakan In sha Allah.

“Shi ma zan yi masa magana kamar yadda nayi magana da gwamna Zulum ɗazun nan.

“Allah ya jiƙansu, ya kuma kawo mana ƙarshen wannan bala’in”.

Arewacin Najeriya dai na fama da matsanancin matsalar rashin tsaro da ta haɗar da Boko Haram, ƴan bindiga daɗi, ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Rahotanni daga ƙididdigar baya bayan nan sun nuna cewa an yi garkuwa da fiye da mutane 1,500 a arewacin Najeriya baya ga biyan ɗimbin kuɗaɗen fansa.

Kazalika, rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 36,000 rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukansu tun daga shekarar 2009, da ƙungiyar ta ɓulla, zuwa yanzu.

Kazalika ayyukan ƙungiyar sun tilastawa sama da mutum miliyan biyu barin muhallansu, inda ƴan Najeriya 240,000 suka yi gudun hijira zuwa maƙwabtan ƙasashe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here