Sauyin Yanayi na ƙara Yaɗa Cutar Zazzabin Cizon Sauro – Rahoto
Wani sabon rahoto ya yi gargaɗin cewa sauyin yanayi na ƙara yaɗa cutar Malaria, musamman yadda aka fuskanci tsananin zafi a sassa daban-daban na duniya.
Read Also:
Rahoton da Global Fund ta fitar, ya zo daidai da ranar da MDD ta ware domin tattauna batun zazzabin cizon sauro.
Mummunar ambaliyar ruwa da aka fuskanta a Pakistan, ta kara yaɗa sauro a sassan ƙasar, kuma sama da mutane miliyan 1,600 ne suka kamu da cutar Malaria a faɗin ƙasar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ƙasashen Afirka na fuskantar ƙaruwar malaria, daga kashi 95 a shekarar 2021 zuwa kashi 96, inda kuma ta ce yara da mata masu juna biyu ne za su fi shan wuya.