‘Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da ‘Yan Kasuwa 50 a Jihar Zamfara
Wani abun bakin ciki ya sake samun Najeriya bayan an yi garkuwa da wasu yan kasuwa 50 a Gusau, jihar Zamfara.
An tattaro cewa mutanen da abun ya ritsa da su san kasance yan kasuwa da ke sayar da wayoyi a wata shahararriyar kasuwar wayoyi ta Bebeji Plaza.
Sai dai kuma, gwamnatin jihar Zamfara da rundunar yan sanda basu fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da lamarin ba.
Zamfara – Wani rahoto da ke zuwa mana ya tabbatar da sace matasa akalla guda 50 a hanyar Sokoto-Gusau a ranar Asabar, 11 ga watan Yuni.
Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, yawancin mutanen da aka sace yan kasuwa ne da ke sana’ar siyar da wayoyi a shahararriyar kasuwar nan da Gusau da ake kira Bebeji Plaza.
Read Also:
An kuma tattaro cewa lamarin ya afku ne da yamma yayin da mutanen da aka sace ke a hanyarsu ta komawa Sokoto inda suka halarci daurin auren daya daga cikin abokan sana’arsu.
Wani ganau ya ba da labarin lamarin
Da yake tabbatar da lamarin ga wakilin Legit.ng, daraktan hulda da jama’a na kungiyar yan kasuwar Bebeji Plaza, Zulkifilu Muhammad wadanda lamarin ya ritsa da su suna tafiya a motocin basu uku lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kama su a kusa da garin Tureta hanyar Sokoto/Zamfara, iyakar jihohin biyu.
Wani mai suna Usman ya fada ma Legit.ng cewa ya shiga dimuwa kan lamarin yayin da yake kuma rokon gwamnatin jihar Zamfara da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa don ceto wadanda aka sace cikin gaggawa.
Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin yan sanda jihar Zamfara, SP Shehu Muhammad kan lamarin ya ci tura domin ba a same shi ba kan layin waya a daidai lokacin kawo wannan rahoton.