‘Yan Bindiga ba su Cancanci Rayuwa ba – Sarkin Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Usman, ya ce babu abin da ‘yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma suka cancanta face mutuwa.
Sarkin na magana ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a ranar Talata a Katsina.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, da wasu da dama.
Read Also:
Sarkin ya ce tunda ‘yan fashin sun yanke shawarar daukar rayukan mutane, su ma “ba su cancanci rayuwa ba”.
Hakazalika ya koka kan jinkirin gurfanar da masu laifi da hukunta su, yana mai cewa “wannan bai dace ba.
A cewar sarkin, dole ne gwamnatoci a dukkan matakai su tashi tsaye su hukunta ‘yan fashin yadda ya dace.
‘Yan ta’adda sun jefa jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya cikin kangi, yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, kashe mutane da kona al’ummomin karkara ya ta’azzar” inji sarkin.