‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan ‘Dan Takarar Gwamnan Jahar Ribas, Tonye Princewill
Tonye Princewill, dan takarar gwamnan Jihar Ribas ya zargi wasu ‘yan bindiga da kai wa gidansa farmaki sai dai basu sace wani abu mai tsada ba.
Kamar yadda ya shaida, sun kai farmakin ne gidansa ne da ke GRA a Port Harcourt da safiyar Juma’a inda suka bincike dakin da suke zargin nashi ne.
Harin ya biyo bayan kwana 4 da ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Rivers – Wani dan takarar gwamnan Jihar Rivers, Tonye Princewill ya zargi wasu ‘yan bindiga da ba san ko suwaye ba da afkawa gidansa amma ba su taba wani abu mai tsada baya, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, ‘yan bindigan sun kai hari gidansa da ke GRA a Port Harcourt da safiyar Juma’a inda suka bincike duk dakunan da suke zargin na dan takarar ne.
Lamarin ya biyo bayan kwana hudu da Princewill ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2023 da ke karatowa karkashin jam’iyyar APC.
A cewarsa an yi yunkurin ganin bayansa ne
Read Also:
Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, a wata takarda wacce Princewill ya daki ranar Juma’a ya kwatanta harin a matsayin yunkurin halaka shi.
Yayin da ya alakanta harin da zabe mai zuwa, ya ce ‘yan bindigan basu taba komai ba sai rakodar CCTV da suka sace wanda hakan ke nuna sun yi yunkurin ganin bayansa ne.
Kamar yadda takardar ta zo:
“Ina tabbatar muku da cewa da safiyar nan aka balle gidana. Alamu sun nuna cewa ni suka yi yunkurin halakawa saboda dakin da suke zargin nawa ne suka balle amma ba su gan ni ba.
“Ba su dauki komai ba sai rakodar CCTV wanda hakan ke nuna ni kadai suka so halakawa. Amma muna godiya ga Ubangijin da ya kare ni.”
Ya zargi wasu ‘yan siyasa
Kamar yadda The Punch ta ruwaito, Princewill ya ci gaba da cewa:
“Hakan na nuna cewa rububin zaben 2023 ya fara matsowa kuma wasu suna iyakar iyawarsu don ganin sun samu mulki. A baya hakan ya yi aiki amma banda yanzu.”
Ya ce ko kadan bai razana da harin ba, zai kara kaimi wurin ganin ya kai inda yake son zuwa. Kuma ya yi fatan Ubangiji ya fallasa wadanda suka kai masa harin.
Yayin da ya bukaci addu’a daga jama’a, ya ce yanzu haka jami’an tsaro suna bincike akan harin kuma yana da tabbacin za su yi iyakar kokarinsu.