Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Jahar Imo
Rahoton da muke samu daga majiya ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki jihar Imo jiya Lahadi.
Wannan harin ya biyo bayan kisan gilla da aka yiwa wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, amma an ce mutane da dama sun jikkata.
Jihar Imo – Rahoto ya bayyana cewa an kashe wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
TheCable ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai farmaki karamar hukumar ne a ranar Lahadi da yamma, inda suka bude wuta kan fararen hula kafin jami’an tsaro su yi kicibis da su.
Read Also:
Mike Abattem, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Imo, har yanzu bai amsa kiran da aka yi masa don tabbatar da faruwar harin ba.
Wani rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ya ce, jami’an tsaro da ‘yan bindiga sun yi artabu a yankin.
A ‘yan watannin nan dai jihar ta sha fama da hare-hare da dama daga ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba.
Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da aka harbi wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karamar hukumar Ihitte Uboma da ke jihar.
Wasu jami’an INEC guda biyu ne aka bayyana bacewarsu a harin wanda ya faru a ranar Alhamis din da ta gabata. Amma daga baya aka same su.
Sakamakon wannan lamari ne hukumar ta INEC ta dakatar da ci gaba da gudanar da rijistar masu kada kuri’a a karamar hukumar.