‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Kwalejin Sojoji dake Jaji a Jahar Kaduna

 

Yan bindiga sun shiga garkuwa da mutane a barikin Sojoji.

Wannan ya biyo bayan sace daliban makarantar FCFM dake Afaka Wasu yan bindiga yanzu haka sun kai farmaki kwalejin Sojoji dake gari Jaji, karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna.

A cewar Daily Trust, wasu mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigan sun je garkuwa da wasu ma’aikatan kwalejin ne da kuma mazauna garin.

Kwalejin horon Sojin Jaji shahrarren makaranta ne da ake horon Sojojin kasa, na sama da kuma na ruwa.

Wani mazauni gairn mai suna Adamu, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindigan sun dade suna addaban mazauna kwalejn da kauyukan dake makwabtaka da kwalejin.

“Allah kadai ke karemu. Sun dade suna kwace masa shanu. Sojoji na bude musu wuta shi yasa basu samun kashe mutane,” Adamu yace.

Kwamandan kwalejin, Air Marshal Olayinka Alade, ya tabbatar da hakan ranar Laraba a Abuja yayinda ya kai ziyara hedkwatar Soji domin ganawa da shugaban hafsan Soji, Laftanan Janar Attahiru Ibrahim. Kwamandan ya ce a ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, yan bindiga sun kora wasu shanu a bayan kwalejin bayan musayar wuta da Sojoji.

Yace: “Ko jiya (Talata), na samu labarin wasu yan bindiga sun kora shanu a bayanmu. Wasu hafsoshinmu na atisaye a wajen. Sun yi arangama da yan bindigan kuma sai da sukayi musayar wuta a lokacin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here