‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Wani Dan Majalisa
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Taraba, Honarabul Bashir Mohammed.
‘Yan bindigan sun bi Mohammed har gidansa ne a cikin dare suka yi awon gaba da shi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tace tana kokarin ceto shi.
‘Yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace dan majalisar Jihar Taraba, Bashir Mohammed.
An sace Mohammed wanda ke wakiltar mazabar Nguroje a majalisar jihar misalin karfe 1 na daren ranar Laraba a Jalingo babban birnin jihar Taraba.
Read Also:
The Cable ta ruwaito cewa an sace dan majalisar ne a gidansa da ke kusa da ofishin hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun shafe kimanin mintuna 45 suna harbe harbe a yayin da suka afka gidansa.
Wata majiya tace yan bindigan ba su taba kowa ba a gidan dan majalisar. Dan majalisar shine mai magana da yawun majalisar jihar a halin yanzu.
Da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, David Misal ya ce rundunar tana kokarin ganin ta ceto Mohammed.
“Mun san abinda ya faru kuma muna kokarin ganin mun ceto shi,” a cewar Misal cikin sakon kar ta kwana da ta aike wa majiyar Legit.ng.