Ƴan Bindiga Sun yi Garkuwa da Dagacin Sabon Birni na Jihar Sokoto

 

Wasu da ake zargin ƴan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Isa Bawa tare da ɗansa a karamar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Ahmed Rufa’i ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels afkuwar lamarin, inda ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike.

Wani babban ɗa ga dagacin Isa Gobir ya ce an yi wa mahaifin nasa kwantan-ɓauna a yankin Kwanar Maharba yayin da yake komawa garinsa na karamar hukumar Sabon Birni daga Sokoto.

“‘Ƴan bindigar sun fara harbi kan mai uwa da wabi lokacin da suka hangi motar mahaifin namu, abin da kuma ya janyo fashewar tayoyin motar da karkatar da hankalin direbansa har ta kai ya tsaya,” in ji ɗan dagacin.

Don haka, Isa ya yi kira ga gwamnati da ta yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da sakin mahaifinsu.

Majiyoyi daga Sabon Birni sun ce lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma damuwa tsakanin mazauna birnin waɗanda ke kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki.

Sun kuma ce an yi garkuwa da ƙarin mutum biyar a yankin a ranar da aka ɗauki dagacin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here