‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Wani Dagaci, Matan Aure  da’Yan Mata

 

Yan bindiga sun sace mai unguwa da wasu mutane 15 a kauyen Kaigar Malamai da ke Jihar Katsina.

Cikin wadanda aka sace akwai matan aure shida, sai ‘yan mata uku da kuma kananan yara guda uku.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar SP Isah Gambo ya ce zai bincika ya tabbatar da gaskiyar lamarin.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a daren ranar Litinin sun sace dagacin kauyen Kaigar Malamai, a karamar hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina tare da wasu mutane 15.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa ‘yan bindigan masu yawa sun afka kauyen a daren ranar Litinin inda suka ci karensu ba babbaka na tsawon awanni kafin suka tafi da wadanda suka sace.

“Sun kai hari kauyenmu, Unguwar Malamai, misalin karfe 11:45 na dare suka fara harbe harbe.

“Sunyi awon gaba da mutane 16 ciki har da dagacin kauyen, Maiunguwa Kabir, matan aure shida, ‘yan mata uku da yara shida.

“A lokacin, mutum uku cikin yan bindigan ya tilastawa daya daga cikin mutanen ya kai su gidan yayansa, a kan babur dinsa, kuma ya aikata hakan.

Biyu daga cikinsu suka shiga gidan daya kuma da ya tsaya daga kofa ya fada wa mutumin ya tsere.

“Da ya tsere daga wurin, ya tafi wurin jami’an tsaro ya fada musu abinda ke faruwa a kauyen amma a maimakon su tafi su tunkari ‘yan bindigan sai suka fada masa ya tsaya a wurinsu ya kwana,” in ji majiyar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar, SP Isah Gambo, ya ce bai riga ya tabbatar da afkuwar abin ba amma ya yi alkawarin zai kira sai dai bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here