‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da ‘Dan Uwan Sakataren Gwamnatin Katsina
Matsalar ‘yan bindiga na cigaba da munana a jahar Katsina, mahaifar shugaban kasa.
Duk da sabbin dokokin da gwamna Masari ya sanya, ana cigaba da sace mutane.
Gwamna Masari ya kalubalanci hukumar ‘yan sanda.
Katsina: ‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.
Read Also:
Katsina Post ta rawaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jahar.
Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba.
Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.
Kabir Muhammad Burkai dai tsohon jami’in dan sanda ne da yayi ritaya kuma manomi ne.
Yana zaune ne da iyalan sa a garin Danmusa.