Ƴan Bindiga sun yi Awon Gaba da Gomman Fasinjoji a Habasha
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da gomman fasinjoji da suka taso daga Addis Ababa, a yankin Oromia da ke ƙasar Habasha.
Lamarin ya auku ne a Ali Doro, kusa da inda aka sace ɗaliban jami’a kusan 100 a lokacin da suke hanyar komawa ɗakunan kwanansu a watan Yulin bara.
Read Also:
Waɗanda suka tsira da hukumomin yankin sun ɗaura alhakin sace fasinjojin a kan ƙungiyar Oromo wato OLA, wadda ta ƴantawaye ce da suke da ƙarfi a yankin.
Sai dai ƙungiyar ta fito ta musanta zargin, inda ta ce ba ta da hannu a lamarin.
Ta ce ita ma ta samu labari, amma “za ta gudanar da bincike.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton gwamnatin ƙasar ba ta ce komai ba.
Garkuwa da mutane – ciki har da fasinjoji – ya fara zama ruwan dare a yankin, inda suke sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.