‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Jigon PDP na Jahar Edo, Owere Dickson

 

Rahotanni sun bayyana cewa an sace wani jigon jam’iyyar PDP kuma jagoran jam’iyyar a gundumar Sanatan Edo ta Kudu, Owere Dickson Imasogie tare da direban sa a safiyar yau.

An yi garkuwa da jigon ne a kan hanyarsa ta zuwa gonarsa lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane suka kama shi da misalin karfe 7 na safe, The Sun ta rawaito.

Wata majiya kusa da danginsa ta ce:

“An yi garkuwa da shi a gonarsa da ke kewayen yankin Obada a karamar hukumar Uhunmwonde. Yana tare da direbansa lokacin da lamarin ya faru.”

A lokacin shigar da wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda ba ta tabbatar ko ta yi wani bayani kan lamarin ba amma wata kungiya, Edo State Decide Movement, a cikin wata sanarwa, ta yi kira ga gwamnan jahar, Godwin Obaseki da ya ceto Owere Dickson.

A wani bangare na sanarwar, kungiyar ta ce:

“Cikin gaggawa, muna kira ga gwamnatin jahar ta Godwin Obaseki da ta dauki kwakkwaran mataki na ceto uban ga kowa da kowa daga hannun ‘yan bindiga ko masu garkuwa da mutane wadanda makiyan ci gaba ne a jahar mu mai kaunar ci gaba.”

Karin bayani na nan tafe..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here