ƴan Bindiga Sun yi Garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga
Jihar Katsina – A wani al’amari mai ban tsoro, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina.
Jaridar Leaderhsip ta tattaro cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar dare lokacin da ‘yan bindigar suka afka yankin.
Read Also:
Harin ƴan ta’addan da sace babban mutum irin Maharazu Tsiga ya haifar da firgici da tashin hankali ga mazauna yankin gaba ɗaya.
Wasu da suka san yadda harin ya afku sun bayyana cewa tuni aka sanar da hukumomin da abin ya shafa kuma jami’an tsaro suna aiki tukuru domin ceto waɗanda aka sace.
Har zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto, babu wasu cikakkun bayanai kan adadin sauran mutanen da suka fada hannun ‘yan bindigar.
Karin bayani na nan tafe…