‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Matafiya a Hanyar Katsina Zuwa Jibia

 

Wasu ‘yan bindiga a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya,sun sace matafiyan da ba a san adadinsu ba a kan hanyar Katsina zuwa Jibia.

Wasu mazauna wurin da lamarin faru, sun shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun isa wurin ne a kan babura kuma sun rika yin harbin kan mai-uwa-da-wabi, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da kuma raunata wasu fasinjojin da dama.

Lamarin dai ya faru ne a daidai kauyen Kadobe, kusa da wani wuri da ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka kafa shingen bincike.

Da da misalin karfe biyar na yammacin Lahadi ‘yan bindigar suka kai hari wajen,amma kuma wasu matafiyan sun samu sun tsere.

Mazaun yankin na Jibia dai na koka wa kan karuwar hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan matafiya da mazauna karamar hukumar lamarin da suka alakanta da hijirar da ‘yan bindigar ke yi daga jIhar Zamfara mai makwabtaka saboda abin da suka kira “sulhun da gwamnatin Zamfarar ke yi da ‘yan bindiga a jihar.

Sun kuma ce wannan lamarin ya fi karfin gwamnatin Katsina, saboda haka suke bukatar gwamnatin tarayya da ta dauki karin matakan inganta tsaro a yankin

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here