‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Matan Aure 3 da Namiji 1 a Jahar Kaduna

 

Wasu mahara da ake zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari yankin Zango da ke yankin Samaru a Karamar Hukumar Sabon Gari, Jahar Kaduna.

A cikin haka suka yi garkuwa da wasu matan aure uku tare da wani namiji daya.

An tattaro cewa ‘yan bindigan sun isa yankin ne da tsakar daren Alhamis, suna ta harbe -harbe.

‘Yan bindiga sun sace matan aure uku da wani mazaunin unguwar Zango a karamar hukumar Sabon Gari ta jahar Kaduna.

Garin Zango yana makwabtaka da Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, jahar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan bindigan sun isa yankin ne da tsakar daren Alhamis, suna ta harbe -harbe.

Lamarin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ‘yan bindiga suka afkawa makarantar horar da sojoji ta Najeriya (NDA), inda suka kashe jami’ai biyu tare da yin garkuwa da wani babban soja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da harin amma ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayanai ba kan lamarin, Aminiya ta rawaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here