Sabon Hari: ‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mutane 36 a Jihar Kaduna
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai farmaki wani yankin jihar Kaduna.
An tattaro cewa, sun hallaka wasu mutane a coci kana suka sace wasu bayan sace ababen hawa da kayayyaki.
Ya zuwa yanzu, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ta Kaduna ya yi tattaki zuwa yankin domin jajantawa da nemo mafita.
Kajuru, jihar Kaduna – Akalla mutane 36 ne aka ruwaito an yi garkuwa da su a wani harin da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna ranar Lahadi.
Mazauna kauyukan ne suka bayyana hakan a wata ganawa da jami’an tsaro a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.
Mazauna yankin sun ce hare-haren da ake kai wa a kai a kai ya shafi rayuwarsu, domin ba za su iya zuwa gonakinsu ba a halin yanzu don gudun kada ‘yan bindiga su kashe su.
Sun kuma ce suna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Kajuru domin ita kadai ce hanyar da za a magance matsalar tsaro.
Read Also:
Wani ganau kuma mazaunin kauyen Kufana, Bashir Bawo, ya bayyana cewa:
“Sa’ad da suka zo, suka hadu da wasu mutane a cikin coci; sai suka yanke shawarar shiga cocin, suka kwashe wasu daga cikinsu, suka tattara su a wani wuri, suka tafi wani kauye.”
A cewarsa, ‘yan bindigan sun zo ne a kan babura inda suka kara sace babura daga mutanen kauyen domin su tafi da wasu mutane.
Ya ce sun kashe wasu daga cikin mutanen kauyen da suka yi kokarin dakile harin kana sun jikkata wasu, rahoton This Day.
Gwamnatin ta kai ziyarar duba Kufana
Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a ranar Litinin, ya jagoranci jami’an tsaro zuwa gundumar Kufana domin samun cikakken bayani game da harin tare da tattaunawa da jama’ar kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Ayoku, da sauran shugabannin hukumomin tsaro na jihar, da shugabannin al’umma, da shugaban karamar hukumar Kajuru.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan ta’addan suka kai hari kan wasu al’ummomi hudu inda suka kashe wasu masu ibada uku daga coci guda biyu tare da kwashe wasu mazauna wurin.