’Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mutum 22 a Katsina
’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 22 a garin Runka da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar Katsina a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rahotanni sun ce maharan sun afka masu ne tsakar dare lokacin da yawancin jama’a ke barci.
Read Also:
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hon. Abdul Jalale Haruna Runka ya ce: ‘“Abubuwa ne gasu nan babu daɗi, ana ta ƙoƙarin tattarewa amma mu kanmu abin ya ɗaure mana kai saboda duk wani inda muke samun bayanai cewa gasu nan zasu fito, babu wani bayani da aka samu kamar yadda aka saba a baya idan suka shirya kawo mana hari. Wannan kawai sai dai aka gan su a tsakiyar gari”.
Ya yi bayanin cewa a yanzu sun duƙufa domin nazarin yadda lamarin ya faru da kuma irin matakan da ya dace a ɗauka a kai.
Shu kuwa Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Safana, Abdullaye Sani Safana, ya ce yanzu haka suna da tabbacin cewa maharan suna riƙe da mutum 22.
Ya kuma ce, “Da farko ma sun fi haka, amma akwai waɗanda suka dawo cikin dare da kuma safiyar Lahadi, daga cikinsu”
Ya kuma bayyana yaƙinin cewa al’umma za su ci gaba da bayar da haɗin kai da goyon baya domin ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa dasu.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce tuni aka jibge jam’an tsaro domin aikin kwato mutanen da kuma tabbatar da ba a sake samun irin hakan ba a nan gaba.