‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4 Sun Kuma yi Garkuwa da Mutane 50 a Jahar Zamfara

 

‘Yan bindiga sun afka garin Goron Namaye sun kashe mutum hudu sun sace 50 a Zamfara.

Rundunar yan sandan jahar Zamfara ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu ta tabbatar da hakan.

Kakakin yan sandan ya ce kwamishinan yan sanda ya tura jami’ai domin ceto wadanda aka sace tare da tabbatar da doka da oda.

Yan bindiga sun kashe mutane hudu sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen 50 a garin Gora Namaye da ke karamar hukumar Maradun na jahar Zamfara kamar yadda yan sanda suka sanar a ranar Litinin.

Daily Trust ta rawaito cewa jami’in hulda da mutane na rundunar yan sandan jahar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Litinin a Gusau.

Shehu ya ce maharan, sun zo da dimbin yawa sun kutsa garin da tsakar daren ranar Lahadi, suka kashe mutane hudu sannan suka sace mutane 50, The Cable ta rawaito.

Wane mataki rundunar yan sanda ta dauka?

Kazalika, ya ce an tura jami’an yan sanda na musamman zuwa yankin a halin yanzu.

A cewarsa, Kwamishinan yan sandan jahar, Yakubu Elkana, ya bada umurnin a fara aikin ceto wadanda aka sace nan take.

Kakakin rundunar yan sandan ya ce kwamishinan ya bukaci mutanen yankin su kwantar da hankulansu a yayin da rundunar ke aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda a garin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here