‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Shugaban CAN na Shiyyar Jos
Daga karshen makon jiya zuwa yanzu, an dauke malaman addinin kirista biyar a Oyo, Kogi da Jos.
A jihar Filato, ‘Yan bindiga sun je har gida ne sun yi awon-gaba da shugaban CAN a shiyyar Jos.
Bayan haka an dauke Fastoci uku da ke yawon wa’azi a Lokoja, an nemi N80m kafin a fito da su.
Plateau – ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kungiyar Kiristoci watau CAN na reshen karamar hukumar Jos ta gabas da ke jihar Filato.
Rahoton da mu ka samu daga The Nation ya nuna an dauke James Kantoma ne da tsakar dare zuwa safiyar jiya, ranar Litinin 13 ga watan Yuni 2022.
James Kantoma shi ne babban Faston cocin St. Anthony Parish da ke kauyen Angware, garin Jos.
‘Yan bindiga sun je har gida sun dauke wannan malamin addini ne kamar yadda shugaban CAN na Filato, Polycarp Lubo ya shaidawa ‘yan jarida.
Shiru har yanzu – Shugaban CAN
Read Also:
Rabaren Polycarp Lubo ya fadawa manema labarai a garin Jos cewa tun da ‘yan bindiga suka yi gaba da Polycarp Lubo, ba su sake jin labarinsa ba.
Kakakin ‘yan sanda na jihar Filato, Alabo Alfred ya ce jami’an tsaro sun san da wannan labari, kuma sun aika dakaru zuwa wurin domin ceto shi.
An sace Fasto a kan hanya
Ana haka ne kuma labari ya zo daga The Cable cewa wasu ‘yan bindigan sun yi gaba da Oluwaseun Aderogba wanda babban Fasto ne a Kwara.
Miyagun sun yi gaba da Limamin na darikar Angilikan ne tare da mai dakinsa da direbansa yayin da suke hanyar zuwa Jebba a kan titin Oyo/ Ogbomoso.
Jami’an tsaro sun ce an sace wadannan mutane da kimanin karfe 8:30 na yammacin Litinin.
Masu wa’azi sun fada hannu
Shugaban kungiyar CEM ta masu kiran yara zuwa ga addinin Kiristanci a jihar Kogi, Charles Esho ta ce an sace masu Fastoci uku a karshen makon jiya.
Vanguard ta rahoto Charles Esho tana cewa ‘yan bindiga sun sace Peter Adigidzi, Fasto Mike Baba da Fasto Sunday Abah yayin da suke kan aiki a Lokoja.
Wata majiya ta ce ‘yan bindigan da suka yi wannan danyen aiki sun bukaci a biya fansar N80m.