‘Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Wani Dan Majalisar Wakilai, Sunyi Garkuwa da Biyu

Har yanzu ‘yan bindiga na cigaba da kai hare-hare tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su a sassan jihar Katsina.

A wannan karon, ‘yan bindigar sun afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai daga jihar Katsina.

‘Yan bindigar sun yi awo gaba da biyu daga cikin ‘yan uwan dan majalisar bayan basu samu mahaifiyarsa ba.

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga a Katsina suka afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kusada/Inagawa/Kankiya tare da yin awon gaba da mutane biyu daga gidan.

Mazauna garin sun sanar da cewa ‘yan bindigar sun fara tambayar ina mahaifiyar dan majalisar bayan sun shiga gidan.

Daga baya ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ‘yan uwan dan majalisar guda biyu bayan sun gaza samun mahaifiyarsa.

Kazalika, ‘yan bindigar sun raunata daya daga cikin ‘yan uwan dan majalisar mai suna Jamilu yayin da ya yi yunkurin tserewa.

Majiya masu yawa, da ke da kusanci da dangin dan majalisar, sun ce Honarabul Kusada da mahaifiyarsa basa garin yayin da ‘yan bindigar suka dira gidan.

Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa dan majalisar, wanda ke Katsina a lokacin da abin ya faru, ya koma Abuja bayan ya sanar da faruwar lamarin a babban Ofishin ‘yan sanda da ke Kusada.

Ba’a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isa, ba a kan batun saboda ba’a same shi ba da aka kira lambar wayarsa ta hannu ba.’Yan Bindiga Sun Shiga Gidan Wani Dan Majalisar Wakilai, Sunyi Garkuwa da Biyu

Har yanzu ‘yan bindiga na cigaba da kai hare-hare tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su a sassan jihar Katsina.

A wannan karon, ‘yan bindigar sun afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai daga jihar Katsina.

‘Yan bindigar sun yi awo gaba da biyu daga cikin ‘yan uwan dan majalisar bayan basu samu mahaifiyarsa ba.

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga a Katsina suka afka gidan Abubakar Kusada, mamba a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kusada/Inagawa/Kankiya tare da yin awon gaba da mutane biyu daga gidan.

Mazauna garin sun sanar da cewa ‘yan bindigar sun fara tambayar ina mahaifiyar dan majalisar bayan sun shiga gidan.

Daga baya ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ‘yan uwan dan majalisar guda biyu bayan sun gaza samun mahaifiyarsa.

Kazalika, ‘yan bindigar sun raunata daya daga cikin ‘yan uwan dan majalisar mai suna Jamilu yayin da ya yi yunkurin tserewa.

Majiya masu yawa, da ke da kusanci da dangin dan majalisar, sun ce Honarabul Kusada da mahaifiyarsa basa garin yayin da ‘yan bindigar suka dira gidan.

Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa dan majalisar, wanda ke Katsina a lokacin da abin ya faru, ya koma Abuja bayan ya sanar da faruwar lamarin a babban Ofishin ‘yan sanda da ke Kusada.

Ba’a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isa, ba a kan batun saboda ba’a same shi ba da aka kira lambar wayarsa ta hannu ba.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here