Jaruma Hadiza Gabon Ta Gina Masallaci

A daren Ranar Asabar ne wani Kabir Idris Kura ya yi wata wallafa a kan jaruma Hadiza Gabon a Instagram.

Ya sanar da yadda jarumar ta dauka nauyin ginin katafaren masallaci tun daga tushensa har zuwa kammalarsa.

A wallafar, ya sanar da yadda jarumar ta bukaci a sirranta amma ya ce zai fi idan ya bayyana alherin jaruman fim.

A daren ranar Asabar ne wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram mai suna Kabir Idris Kura ya wallafa bidiyon wani masallaci da aka fara gininsa tun daga tushe har aka kammala shi.

Bawan Allan ya wallafa, “Alhamdulillah, wannan ne masallacin da jaruma Hadiza Gabon ta ginawa bayin Allah domin yin sallah fisabilillah.

“Ginin ya kammala kuma muna mata addu’ar Allah ta’ala yasa mata a mizaninta, ya kuma saka mata da alkhairi, ya ji kan mahaifinta Malam Aliyu Diya.

“Ki gafarceni mamana da wannan wallafar. Jama’a da dama sun san sharrin ‘yan fim, ya kamata su san alkhairinsu”

Alamu na nuna cewa wanda ya wallafa wannan bidiyon dan masana’antar ne domin sunan shafinsa na Instagram yana da alaka da kamfanin shirya fina-finai na two effects.

Haka zalika, alamu na nuna shine mamallakin kamfanin ginin da ya karba kwangilar ginin masallacin.

Hakan ne yasa ya bugi kirji ya nuna wa duniya irin alkhairin ‘yan fim duba da yadda suka yi kaurin suna a idon duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here