‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manyan Jami’an Sojoji 22 a Jihar Delta
Wasu ƴan bindiga sun yi wa sojoji kwanton ɓauna a ƙauyen Okuoma da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta, inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Rundunar soji ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, inda ta sha alwashin bin diddigin wasu matasa, waɗanda suka farmaki sojojin.
Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Tukur Gusau, ya ce wasu matasa ne a ƙaramar hukumar Bomadi ta jihar ɗauke da makamai suka farmaki sojojin tare da halaka su.
Asaba, jihar Delta – Aƙalla sojoji 22 ne wasu ƴan bindiga a ƙauyen Okuoma suka halaka a ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sojojin na Bataliya ta 181, Bomadi, sun je aikin ceto ne a lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna a ranar Alhamis 14 ga watan Maris.
Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya fara ne a ranar Alhamis lokacin da sojojin suka samu kiran gaggawa kan rikicin ƙabilanci da ya ɓarke tsakanin mutanen ƙauyukan Okuoma da Okoloba.
Yadda aka yi wa sojojin kwanton ɓauna
Read Also:
Sun je aikin ceto ne a ƙauyen Okuoma domin kuɓutar da wani matashi, Mista Anthony Aboh, na ƙauyen Okoloba a ƙaramar hukumar Bomadi wanda aka sace saboda rikicin filin da ake yi tsakanin ƙauyukan.
Wani majiya ya ce an mamayi sojojin ne lokacin da suke dawowa bayan sun gama tattaunawar da bata haifar da ɗa mai ido ba kan matashin a ɗakin taro na ƙauyen Okuoma.
“Mutane da dama aka halaka da suka haɗa da wani tsohon ɗan majalisa daga ƙauyen Okoloba wanda ya kai rahoton lamarin ga JTF.
“Amma, kwamandan da sauran sojojin an yi garkuwa da su ne, inda aka kai su wani ɓoyayyen waje kusa da ƙauyen da ke makwabtaka.
Sojojin da aka kashe
Majiyar ya ƙara da cewa an tabbatar da halaka sojoji 22 a ƙauyen Okuoma.
Daga cikinsu akwai Laftanar Kanal ɗaya, Manjo biyu, Kyaftin ɗaya da sojoji 18.
Wasu daga cikin sojojin da aka kashe sun haɗa da Manjo Shafa, Manjo Obi, Kyaftin Zakari da Laftanar Kanal A. H. Ali.
Babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa tare da cafke wadanda ke da hannu a wannan ɗanyen aikin.
A wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana hakan, inda ya ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga gwamnatin jihar Delta.