‘Yan Bindiga Sun Halaka Jami’an ‘Yan Sanda Uku a Jahar Abia

 

Miyagun ‘yan bindiga sun halaka jami’an ‘yan sandan uku tare da kwashe makamansu.

Lamarin ya faru ne bayan ‘yan bindigan sun budewa ‘yan sandan wuta a kan titi yayin da suke duba motoci.

‘Yan sandan da aka kashe an bayyana sunansu da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi ‘Yan bindiga sun sheke ‘yan sanda uku a sabon harin da suka kai karamar hukumar Ohafia ta jahar Abia.

The Cable ta gano cewa ‘yan sanda da aka kashe a safiyar Litinin suna kan titi ne yayin da suke duba motoci masu wucewa. An gano cewa ‘yan sandan sun kai harin sannan suka yi awon gaba da bindigogin jami’an tsaron.

‘Yan sandan da aka kashe sun hada da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi.

Ude Chukwu, mataimakin gwamnan jahar, ya kushe wannan harin yayin da ya kai ziyara yankin bayan sa’o’i kadan da aukuwar lamarin.

Ya kara tabbatarwa da mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta tura abubuwan da ake bukata.

Cigaban yazo ne kasa da wata daya bayan kashe wani jami’in dan sanda da aka yi a jahar bayan ‘yan bindiga sun kutsa Aba.

‘Yan bindigan sun yi awon gaba da makamai daga ofishin ‘yan sandan. Lamarin da ya faru na nuna hauhawar rashin tsaro da kuma harin da ake kaiwa jami’an tsaro a yankin kudancin kasar nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here