‘Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamishina a Katsina da Masallata 16 a Jahar Neja
Rahotanni daga jahar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kashe wani kwamshina a jahar Katsina a arewacin Najeriya.
Kwamishinan ƴan sanda na jahar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema labarai a ranar Alhamis. Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.
Sannan wasu rahotannin daga jahar Neja a arewa ta tsakiyar ƙasar kuma ƴan bindigar sun kashe mutum 16 a masallaci wasu goammai kuma sun jikkata a wani hari da ‘aka kai ƙauyen Ba’are a karamar hukumar Mashegu da ke jahar Nejan.
Ahmed Ibrahim Matane shi ne sakataren gwamnatin jahar ta Neja, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar Laraba
Read Also:
Lamarin Katsina
Kwamishinan ƴan sanda ya ce tuni an fara bincike kan mutuwar kwamishinan kmiyya da fasaha na jahar Katsinan, “don haka babu wani dogon bayani da zan iya yi yanzu, sai dai a saurara sai binciken ya yi nisa,” in ji shi.
Ya ce tuni aka kai gawar mamacin asibiti.
Bayanai sun ce an kashe Kwamishina Dr Rabe Nasir ne a gidansa da ke rukunin gidaje na Fatima Shema Estate a cikin birnin Katsina.
Lamarin Neja
Ahmed Ibrahim Matane ya ce an far wa mutanen ne da sanyin Safiya lokacin da suke yin sallar asubahi.
Yace ‘yan bindigar sun zo ne kan babura su fiye da 200 suka far wa wannan kauye.
Ya kara da cewa an girke jami’an tsaro da za su ci gaba da kai kawo domin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Wannan hari na zuwa ne kasa da wata daya da ‘yan bindiga suka kashe wasu masallata 18 a garin Mazakuka a dai karamar hukumar ta Mashegu.
Mashegu dai na daya daga cikin kananan hukumomi jahar Neja wadanda ke kusurwar yankin Kwantagora, da suke kusa da dazukan da wadannan yan bindiga ke da sansanoni.