‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’an ‘Yan Sanda Huɗu a Jahar Enugu

Aƙalla jami’an yan sanda huɗu aka kashe a wani hari da yan bindiga suka kai wurin binciken abun hawa dake yankin Obeagu-Amechi, ƙaramar hukumar Enugu ta kudu, jahar Enugu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Duk da cewa hukumar yan sanda ba ta faɗi adadin waɗanda suka mutu ba, amma wani mazaunin yankin yace yaga gawar yan sanda huɗu bayan harin.

Hakanan wasu mutum biyu da hanya ta biyo da su, cikinsu harda wani Fasto sun rasa rayuwarsu sanadiyyar harin.

Jami’ai sun kashe yan bindiga Yan bindigan sun sake kai hari jim kaɗan bayan faruwar wancan a gadar Inyaba dake kan hanyar Uno-Amodu – Umueze Amechi.

Rahoto ya bayyana cewa aƙalla yan bindiga uku yan sanda suka hallaka a wurin, waɗanda aka sanar da su cikin gaggawa kuma suka kawo ɗauki.

Ruwan wutar da aka yi yayin harin ya bar mutane da dama dake yankin cikin raunuka, sannan maharan sun cinna wa motar sintirin yan sanda wuta.

Yan Sanda sun fara bincike Kakakin yan sandan jahar, ASP Daniel Ndukwe, wanda ya tabbatar da kai harin, ya bayyana cewa:

“Bayanai dangane da musayar wuta da ta faru da yammacin ranar 21 ga watan Yuli, wanda wasu yan bindiga suka kaiwa jami’an yan sanda a wurin bincike dake Obeagu-Amechi, yana da rikitarwa.”

“Amma a halin yanzu mun fara gudanar da bincike kan ainihin abinda ya faru, kumu zamu sanar a hukumance.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here