PDP: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Jigon Jam’iyyar Tare da Garkuwa da Yaransa
Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun jefa al’umman Bosso da jihar Niger cikin rudani da fargaba.
Hakan ya kasance ne sakamakon kisan jigon PDP, da yan bindiga suka yi a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba.
An kuma yi garkuwa da yaran Mohammed wanda ya kasance shahararren dan kasuwa kuma manomi su uku.
Tsoro ya kama mutanen karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger sakamakon kisan Alhaji Ahmodu Mohammed, jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
An tattaro cewa yan bindiga ne suka kashe Mohammed a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, sannan suka yi garkuwa da yaransa mata su uku, jaridar ThisDay ta ruwaito.
Read Also:
A cewar idon shaida wanda ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, ya ce wasu yan bindiga kimanin su 15 sun kai mamaya garin dauke da makamai daban-daban sannan suka fara harbi don tsoratar da mutane.
An ce yan bindigan sun fara kai hari ga yan kasuwa a shahararriyar kasuwar Beji kafin suka zo karamar hukumar Bosso. An ce sun kai ziyara biyu a baya ga jigon PDP a garin.
Koda dai rundunar yan sanda bata riga ta tabbatar da al’amarin ba, wani makusancin marigayin ya ce an shirya kaiwa Alhaji Mohammed hari ne saboda yana da karfi sosai.
“Wannan shine karo na uku da yan bindiga ke kaiwa mutumin harin. Suna ta zuwa a baya amma basu cimma nasara ba saboda mutumin na da karfi.
An harbe shi sau da dama kafin ya mutu.” An binne jigon na PDP a ranar da aka kashe shi daidai da koyarwar addinin musulunci.