‘Yan Bindiga Sun Harbe Babban Jami’in ‘Yan Sanda

 

Wasu miyagun yan bindiga sun tare Jami’in ɗan sanda da ya kai matsayin Insufekta sun harbe shi har lahira a jihar Legas.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, Benjamin Hundeyin, ranar Alhamis.

Ya ce Marigayin ya baro wurin aikin da nufin zuwa wani wuri yayin da aka farmake shi aka harbe shi har lahira da yammacin Laraba.

Lagos – Rundunar yan sanda reshen jihar Legas ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kashe Insufektan yan sanda ranar Laraba a yankin Coker Aguda a jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Alhamis a Legas cewa Jami’in na cikin Keke-Napep lokacin da maharan suka bindige shi.

Kakakin yan sandan ya ce tuni rundunar ta kaddamar da bincike kan lamarin domin bin sawu tare da cafke yan bindigan, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wane matakin rundunar yan sanda ta ɗauka?

Hundeyin ya ce sun kama Direban Keke-Napep ɗin domin amsa wasu tambayoyi amma daga baya sun sake shi da sharaɗin zai dawo ranar Alhamis domin taimaka wa yan sanda kan binciken da suke yi.

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa an tura Mamacin ya yi aiki a wani Banki, amma kaddarar da ta yi ajalinsa ba ta faɗa masa lokacin da yake wurin aikin ba.

“Ya baro wurin aikinsa domin zuwa wani wuri a cikin Keke mai kafa uku. Ya ɗauki shatar Keken ne kuma shi kaɗai ne fasinja a ciki.”

“Ba zato aka farmake shi, aka harbe shi, sannan suka yi awon gaba da bindigarsa ta aiki. Lamarin ya auku da yamma kusan ƙarfe 3:00, ya rasu da daren ranar.”

– Benjamin Hundeyin.

Kakakin yan sandan ya ce ba zasu saki bayanan Mamacin ba har sai sun tuntuɓi iyalansa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here