Ƴan bindiga Sun Kai Hari Asibiti a Jihar Kaduna
Birnin-Gwari, Kaduna – Ƴan bindiga sun kai kazamin farmaki asibitin PHC da ke kauyen Kuyallo a ƙaramar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da ma’aikatan jinya da kuma majinyata da dama a harin na yau Litinin, 9 ga watan Satumba.
The Nation ta ce har kawo yanzu da ta haɗa rahoton babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko rundunar ƴan sanda kan sabon harin.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin baya amsa kiran waya ko sakonni.
Yadda ƴan bindiga suka shiga asibitin
Read Also:
An tattaro cewa maharan sun isa kauyen da karfe 9:00 na safe kuma da farko sun shiga makarantar sakandire ta gwamnati amma suka taras babu kowa.
A cewar shugaban ƙungiyar ƴan banga na yankin, Musa Alhassan, ganin babu kowa a makarantar ne ya sa ‘yan bindigar suka karkata akalarsu zuwa asibitin.
“Sun zo da niyyar farmakar ɗalibai amma da suka ga makarantar babu kowa sai suka wuce asibitin, suka ɗauki mutane,” in ji shi.
Matane nawa aka sace a harin asibitin?
Ganau sun ce maharan na ɗauke da bindigu da adduna a lokacin da suka tattara mutane suka tafi da su a asibitin ciki hada ma’aikatan jinya mata guda biyu.
Har yanzun ba a tantance yawan majinyatan da maharan suka yi garkuwa da su ba a harin wanda ya haifar da firgici da tsoro a zuƙatan mazauna garin, in ji Punch.