‘Yan Bindiga sun kai Hari Asibiti a Jihar Ondo
Wasu ’yan bindiga sun kai hari wani asibiti a Akure, Jigar Ondo, da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka sace ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki.
Rahotanni sun ce maharan sun je ne da mota ƙirar bas, suka kutsa cikin asibitin tare da ɗauke wasu daga cikin ma’aikatan.
Read Also:
Sai dai jami’an tsaron Amotekun a Jihar Ondo sun samu nasarar ceto wasu daga cikin waɗanda aka sace a wasu hare-hare da suka kai cikin dare.
Kwamandan Amotekun, Akogun Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya uku ne aka sace, ba shida ba kamar yadda aka fara ruwaitowa.
Haka kuma, ya ce jami’ansu sun ceto wani mutum da ɗansa da aka sace a daren.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira yin ga al’umma da su riƙa bayar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka.















