‘Yan Bindiga Sun Kai wa Coci Hari a Jahar Lagos

 

Lagos:- Wasu yan bindiga sun kutsa wurin ibadar kirista (Cocin RCCG) sun harbe Fasto Bolanle Ibrahim, har lahira a jahar Lagos.

Dailytrust ta ruwaito cewa an kashe Ibrahim ne akan mumbarin cocin dake Kauyen Maidan, karamar hukumar Ikosi Ketu, jahar Lagos.

Rahoto ya nuna cewa mamacin yana tsaka da addu’a ga wata mata yayin sadaukarwa ga ‘ya’ya lokacin da maharan suka afka cikin cocin.

Yan bindigan sun yi kokarin tafiya da Fasto Ibrahim, amma wani babban fasto na gaba da shi ya dakatar da su da tambayar me suke bukata.

Me yan bindigan suka zo nema?

Yar uwar faston da aka kashe, Mrs. Justina Alebiosu, ta bayyana lamarin da wani shiryayyan kisan kai.

A jawabinta tace:

“Kafin su kashe shi sai da suka nuna masa hotonsa domin ya tabbatar shine suka zo dominsa. Mutuwarsa ta zo mana bagatatan kuma mun yi babban rashi.”

“An haife mu a cikin addinin musulunci amma daga baya muka koma kiristanci, a tunani na ɗan uwa na yana da wata alakar kasuwanci da wani.”

“An faɗa mun cewa yayin da maharan suka yi kokarin tafiya da shi yana tsaka da yiwa wata mata addu’ar sadaukarwa ga ƴaƴanta, sai ya nemi su kashe shi anan kuma suka aikata haka.”

Ta kara da cewa maharan sun yi barazanar harbe duk wani dake cikin cocin idan ya yi kokarin hana su aiwatar da abinda ya kawo su.

A taimaka mana mu binne ɗan uwanmu

Mrs. Alebiosu ta yi kira ga kwamishinan yan sanda na jahar, Hakeem Odumosu, ya taimaka a basu gawar ɗan uwansu su mata jana’iza.

Matar faston, Mrs. Kudirat Ibrahim, ta bayyana cewa da azumi a bakin mijinta a ranar da aka kashe shi.

Mrs. Ibrahim ta kuma musanta jita-jitar da wasu ke yaɗawa cewa mijinta ɗan kungiyar asiri ne kuma kisan shi na da alaƙa da haka. Wane mataki jami’an tsaro suka ɗauka?

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here