‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar ‘Yan Sanda a Jahar Imo

 

Yan bindiga sun kai mummunan hari wata Hedkwatar yan sanda a Imo, mutane yankin sun tsorata sun yi takan su.

Wani mazaunin yankin ya ce Artabun da aka yi tsakankin dakarun yan sanda da maharan ya hargitsa mutane kamar duniya ce zata tashi.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Imo, Abattam, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace zai kara bincikawa.

Imo- Da safiyar Litinin, wasu ƴan bindiga sun farmaki hedkwatar yan sanda dake Otoko, ƙaramar hukumar Obowa a jihar Imo dake kudancin Najeriya.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yan ta’addan sun bar jami’an yan sanda biyu kwance da rauni yayin harin.

Mazauna ƙauyen sun shaida wa manema labarai cewa maharan sun shigo da karfe 3:00 na dare, kuma sun kwashe dogon lokaci yayin harin.

Daily Trust ta rahoto Wani Mutumi ya ce:

“Bamu iya bacci ba da dare, ƙarar tashin makamai babban tashin hankali ne. Yayin da mutane da yawa suka tsere cikin jeji, wasu kuma sun fake a cikin gidajen su.”

“Hedkwatar yan sandan tana kan babbar hanyar Owerri-Umuahia, dakarun yan sanda sun tarbe su, suka fara artabu, komai ya ƙara dagulewa mutanen ƙauyen kai kace duniya ce zata tashi.”

“An yi kazamin musayar wuta da bamu taɓa gani ba, yan sanda biyu sun ji munanan raunuka, yanzu haka an gaggauta kai su Asibiti.”

Maharan sun kwashi kashinsu a hannu

Wata majiya ta daban ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan bindiga kuma ba su samu damar shiga harabar hedkwatar yan sandan ba.

“Yan bindigan sun fuskanci turjiya daga yan sandan dake bakin aiki, ba su iya shiga harabar ba, an yi artabu mai muni. Yan sanda biyu sun jikkata, bansan halin da suke ciki ba.”

“Yanzu da nake magana da ku, an girke jami’an tsaro ta ko ina a yankin. Mutane a tsorace suke, kowa ya yi muƙus a cikin gida, abun dai ba daɗin ji.”

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, da aka tuntuɓe shi yace, “Eh dagaske ne an kai hari,” amma ya yi alkawarin fitar da karin bayani daga baya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here