‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango
Rahoto ya shaida cewa, a daren ranar Laraba ‘yan bindiga sun kai hari gidan Damishi Sango.
Sango ya kasance tsohon ministan wasanni dan asalin jahar Filato a arewacin Najeriya.
A yayin harin an harbe jami’an tsaro biyu da wani yaro, an kuma gudu da bindigigon jami’an ‘Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango, da ke jahar Filato.
Jaridar The Nation ta samu labarin sun kai hari gidan nasa da ke Danwal, Ganawuri bayan Vom, a karamar hukumar Riyom da misalin karfe 9:00 na daren Laraba.
Read Also:
A cewar rahotanni, an harbe wasu jami’an tsaro biyu da wani yaro yayin harin. An kuma fahimci cewa ‘yan bindigar sun tafi da bindigogin jami’an.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Filato, ASP. Gabriel Ubah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce: “Rundunar ‘yan sanda na sane da faruwar lamarin a Riyom kuma an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti inda suke karbar magani.
“Ban sani ba tukuna ko an kwace bindigoginsu.
“Tawagar masu bincike da jami’an leken asiri tuni suka fara bincike tare da farautar masu laifin.”
Ya ba da tabbacin cewa tsohon Ministan da danginsa suna cikin koshin lafiya kuma ba a samu rauni ba.