‘Yan Bindiga Sun Kaiwa Rugar Fulani Hari a Jahar Zamfara

Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wani rugar fulani da ke Anka a jahar Zamfara.

Sai dai jami’an tsaro da aka tura garin sun fatattake su sun kwato shanun da suka sace.

Kwamishinan yan sandan Zamfara ya yabawa jami’an tsaro ya umurci mutane su cigaba da basu hadin kai Yan bindiga sun kai hari a wani rugar Fulani da ke wajen garin Anka a hanyar Bagega zuwa Anka a jahar Zamfara.

Majiyoyi sun shaidawa Channels Television cewa yan bindigan sun kutsa garin misalin karfe 5 na yamma suka fara harbe-harbe ba tare da kakautawa ba.

Sai dai jami’an yan sanda da aka ajiye a wani kamfanin hakar ma’adinai da ke kan hanyar sun tunkari yan bindigan inda suka yi musayar wuta kamar yadda wani ganau ya bayyana a ranar Alhamis.

Ya ce ba a rasa rai sakamakon harin ba amma yan bindigan sun sace shanu da a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba daga mazauna garin. Shaidan ganin idon ya kuma ce yan bindigan sun kona babur din sarkin Fulanin Anka.

Rundunar yan sandan a jahar ta tabbatar da harin tana mai cewa yan sandan sun dakile harin sannan sun kwato shanun da yan bindigan suka sace.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin yan sandan jahar, Shehu Mohammed ya yi bayanin cewa an sanar da yan sandan da aka tura Anka cewa yan bindiga sun kai hari. “Hadakar yan sanda da sojoji da aka tura wurin sunyi musayar wuta da yan bindigan.

“Sakamakon hakan yan bindigan sun tsere sun shiga daji da raunin bindiga,” in ji Mohammed.

Ya kara da cewa, “An kwato dukkan shanun da suka sace a wurin fulanin garin sannan ana cigaba da sintiri domin kare afkuwar wani harin.”

Kwamishinan yan sandan jahar, Hussaini Rabiu ya yabawa jami’an tsaron ya kuma yi kira ga jama’a su cigaba da bawa jami’an tsaron hadin kai.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here